1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Bukatar agaji bayan ambaliya

Zainab Mohammed Abubakar
August 19, 2018

Ruwan sama ya dan tsagaita a jihar Kerala ta kasar Indiya da ta fuskanci ambaliyar ruwa, sai dai yunkurin kai ruwan sha da abinci da magunguna ga sama da mutane dubu 100 da ambaliyar ta rufe a gidajensu ya ci tura.

https://p.dw.com/p/33OOb
Indien Monsun - Überschwemmungen in Kerala
Hoto: Imago/Xinhua

A cewar ministan harkokin noma na Indiyan Sunil Kumar za a yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen sauke kayan abinci ga al'ummar wannan jihar da ke cikin yanayi na tashin hankali. Ya kara da cewar wajibi ne gwamnati ta samarwa mutane kimanin miliyan guda wurin zama, wadanda ambaliyar ta wanke matsugunnansu, wadanda a yanzu haka ke samun mafaka a rumfunan wucin gadi da aka tanada.

Akwai dubban mutane da har yanzu ke makale a saman gidaje da bishiyoyi, a yayin da ake amfani da jiragen sama wajen daukar tsofaffi da yara kanana zuwa sansanonin da aka kebe. Tun daga ranar tara ga watan Agustan da muke ciki ne dai, sama da mutane 350 suka rasa rayukansu daga ambaliyar, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi babu kakkautawa a jihar ta Kerala, inda a halin hanzu lamura suka tsaya cik.