Mutane 5 sun mutu a Indiya sakamakon gobara
May 7, 2020Talla
Jami'an kashe gobara sun baiyana cewar gobarar ta tashi ne sakamakon fitar iskar gas ta wani bututu da ya fashe a wannan lokaci da ake zaman gida. Sai dai hukumar kashe gobarar ta tsoratar game da samun iyalai cikin mawuyacin hali a cikin gidajensu sakamakon shakar iskar gas.
Daga cikin mutanen da ke kwance a asibiti akwai mata da kananan yara, a nata bangaren hukumar yan sanda ta bayyana shirin bi gida-gida domin gano yanayin da makwabtan ma'aijar sinadaran ke ciki.