1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutune 40 sun mutu a hadarin mota a Indiya

Ramatu Garba Baba
July 1, 2018

Hadarin mota ya halaka mutune 40 a yankin Uttarakhand tare da raunata wasu mutanen uku, motar kirar bas mai jigilar fasinja ta saki hanya inda ta fada a wani yankin da ke da tarin tsaunuka.

https://p.dw.com/p/30cNB
Indien Busunfall
Hoto: Getty Images/AFP

Tuni dai masu aikin ceto suka isa wurin don kwashe gawarwaki dama bai wa wadanda suka sami rauni kulawa. Hadarin na zuwa ne, bayan da aka wayi gari a kasar da gano gawarwakin da aka rarrataya a jikin silin na rufin wani gida. 10 daga cikin gawarwakin an rufe musu fuskokinsu. Ba a dai kai ga tantance ko su suka kashe kansu ko kuma kashesu aka yi ba. Ba kuma karin bayani ko mamatan 'yan uwan juna ne.

Amman 'yansanda sun ce ba su ga wata alamar harbin bindiga a jikin kowannensu ba,  Akwai wata dattijuwa mai shekaru kimanin saba'in da biyar daga cikin mamatan 11 da aka tsinci gawarta a gefen dakin.