Indiya: Mahaukaciyar guguwa ta kashe mutane
May 21, 2020Talla
Guguwar wadda aka yi wa lakabi da Amphan ta afkawa gabashin kasar ta Indiya ne musamman ma dai jihar nan ta West Bengal kuma ta fara wannan ta'adi nata ne tun daga jiya Laraba.
Baya ga gabashin Indiya da wannan ibtila'i ya shafa, rahotanni na cewar lamarin ya shafi kasar Bangladesh wadda ke makotaka da kasar ta Indiya inda nan ma guguwar ta yi ta'adi har ma aka bada labarin rasuwar mutum akalla goma.