1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Cutar Nipah ta kashe mutane a Indiya

Gazali Abdou Tasawa
May 22, 2018

Mahukuntan kiwon lafiya a Indiya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane biyar a garin Kerala sakamakon kamuwa da cutar Nipah mai saurin kisa da jemage ke yadawa.

https://p.dw.com/p/2y5Uz
Indien tödliches Nipah-Virus
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Mahukuntan kiwon lafiya a Indiya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane biyar a garin Kerala sakamakon kamuwa da cutar Nipah mai saurin kisa. Kazalika mahukuntan sun sanar soma bincike kan wasu kutane tara masu fama da rashin lafiyar da ake kyautata zaton sun harbu da cutar ce a yayin da aka killace a matakin rigakafi wasu mutanen 94 da suka dafa gawarwakin mutanen da suka mutu bayan kamuwa da cutar ta Nipha wacce ke zama sanannar cuta a yankin kudu da kuma kudu maso gabashin nahiyar Asiya. Cutar Nipha dai wata cuta ce da jemage ke yadawa da kuma ke saurin kisa inda kusan kaso 70 daga cikin 100 na mutanen da ke kamuwa da ita ke shekawa lahira. Kawo yanzu wannan cuta wacce ta taba halaka mutane sama da 100 a kasar ta Bengladesh a shekara ta 2001 ba ta da magani.