1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IMF ta ce tattalin arzikin Nijar ya bunkasa

November 8, 2016

Bankin bada lamuni na IMF ko FMI ya sanar da cewar tattalin arzikin Nijar ya samu cigaba duba da wasu tsare-tsaren da hukumomin kasar suka yi.

https://p.dw.com/p/2SMuy
Niger Präsident Issoufou Mahamadou
Hoto: picture alliance/AP Photo/A. Calanni

Jami'an Asusun Bada Lamuni  na Duniya wato IMF ko FMI da suka yi wata ziyarar aiki ta makonni biyu a Jamhuriyar Nijar suka ce tattalin arzikin kasar ya samu tagomashi idan aka yanzu ya kai kashi 4.5 cikin 100 idan kwatanta shi da yadda ya ke a shekarar 2015 da ta gabata inda ya kasance kashi 3.5 cikin 100. Wannan dai ya sanya IMF din yin alkawarin baiwa Nijar wasu kudade don gudanar da aiyyukan raya kasa.

Wannan cigaban da aka samu dai na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale da dama ciki kuwa har da na tsaro wanda ya durkusar da harkoki na kasuwanci a sassan kasar da dama. Wani abu da ya taimaka wajen cimma wannan nasara da aka yi shi ne wadatar amfanin gona duk kuwa da cewar ba a kammala lissafin abinda aka samu ba.

To sai dai a daura da wannan, masana na ganin cigaban da aka samu ka iya samun koma baya duba da yadda hukumomi ke rushe-rushen shagunan 'yan kasuwa wanda aka gina ba bisa ka'ida ba domin hakan zai iya taimakawa waje yin nakasu ga harkokin kasuwanci da tattalin arziki na kasar.