1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Idriss Deby ya sa ƙafar wando guda da kampanonin haƙo man petur

August 27, 2006
https://p.dw.com/p/BulU

Yau ne wa´adin kwana ɗaya tilo, da shugaban ƙasar Tchad, ya ba kampanonin haƙo man petur, na Chevron da Petronas, na fita daga ƙasar ke kai ƙarshe.

Shugaba Idriss Deby, ya umurci kampanonin 2 mallakar Amurika, da Malaisia, da su gama yanasu, yana su, su fice daga ƙasar Tchad.

Deby ya zargi wannan kampanoni , ba rashin cika alƙawuran da su ka ɗauka, ta fannin biyan kuɗaɗen haraji ga assusun gwamnati.

Wannan hukunci na ba zata, ga kampanonin, ya biwo bayan hurucin shugaban ƙasa, a wannan mako ,inda ya gayyaci kampanonin haƙo mai, na ƙasar su sake laale, ta fannin raban kasson kuɗaɗen albarkatun man petur, inda a cewar Deby, Tchad da dokin ta, ta koma kutur.

Shugaban ƙasa,ya bayyana girka wani saban kampani mallakar Tchad, wanda zai maye gurbin Chevron da Petronas, tare da haɗin gwiwa da kampanin Exxon Mobil shima, na ƙasar Amurika.

A ɗaya hannun kuma, Shugaban ƙasar Tchadi, ya bayyana tsige ministan albarkatun man petur, daga muƙamin sa, tare da zargin sa, da yin kashe mu raba, da kampanonin haƙo mai.

Kazalika, ya bayyana gurfanar da ministan da ya tsige, da magajin sa a kujerar, gaban kotu.