1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Idriss Deby Itno ya yaba kasar France bayan tallafin da ta bashi ya kori yan tawaye

April 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1U

Shugaban ƙasar Tchad Idriss Deby, ya yaba wa ƙasar France, a sakamakon tallafin da dakarun ta, su ka bashi, ya kori yan tawaye, ranar alhamis da ta gabata.

Ya ce Gwamnatin Tchad ta gamsu, da bayyanan sirri, da rundunar tsaron France ta bata, wanda ta hakan ne, sojoji masu biyaya ga gwamnati, su ka samu nasara fattatakar yan tawaye.

Saidai, ya mussasanta zargin da ake, na cewar rundunar France, ta harbi yan tawaye.

Idriss Deby, ya tabatar da cewa, ƙasar sa, zata anfani da kuɗaɗen albarkatun man Petur, domin sayen makamai na zamani,da zumar wanzar da tsaro a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Wannan sa hannu na ƙasar France, a rikicin tawayen Tchad, ya jawo wani saban kace na kace, a fagen siyasar ƙasar Frace, inda jam´iyar yan gurguzu, ta yi Allah wadai da wannan mataki.

Ta kuma yi kira, ga shugaban ƙasa Jaques Chirac, ya tsame hannuwan gwamnatin France, daga rikicin cikin gida na ƙasar Tchad.