ICC za ta dakatar da bincike kan Dafur
December 13, 2014Talla
Fatou Bensouda da ke zaman babbar mai gabatar da kara a kotun ta ICC ta ce wannan mataki da suka dauka ya zama wajibi domin kuwa ya zuwa yanzu babu wanda aka hukunta kana kwamitin na sulhu bai taka wata rawar gani ba wajen taimakawa don kawo karshen laifukan yakin da aka tafka a yankin.
Rikicin yankin Dafur dai na daga cikin batutuwan da aka gabatar gaban kotun ta ICC sakamakon zub da jinin da aka yi cikin shekara ta 2003 lokacin da 'yan tawaye suka yi fito na fito da mahukuntan gwamnatin Sudan wadda Shugaba Omar al-Bashir ke jagoranta.