ICC ta ɗage shari'a shugaban ƙasar Kenya
October 31, 2013Talla
Tun farko an shirya za a gudanar da zaman shari'ar ne a ranar 12 ga watan Nuwamba da ke kamawa a gobe,to amma kotun ta ce lauyoyin da ke kare shugaban ƙasar suka buƙaci a ɗage zaman.
Hakan kuwa ya biyo bayan hare-haren da aka kai a wata cibiyar kasuwancin ƙasar ta Kenya domin bai wa shugaban damar fiskantar lamarin. Ana tuhumar shugaban na Kenya da matamakinsa William Ruto da laifin haddasa tashin hakali da ya biyo bayan zaɓen shekarun 2007. Wanda a cikinsa mutane kusan dubu suka mutu yayin da wasu sama da dubu ɗari shida suka fice daga gidajensu.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman