ICC ta zartar da hukunci a kan Katanga
March 7, 2014Duk da cewar an wanke shi daga zargin fyade da cin zarafin mata ta hanyar bautar dasu da amfani da sanya yara kanana aikin soji, Germain Katanga bai nuna alamun nadama adaidai lokacin da Alkalan kotun ke zartar da hukuncin samunsa da hannu a harin da aka kaiwa kauyen Bogoro a ranar 24 ga ga watan 2003, wanda yayi sanadiyyar rayukan fararen hula 200. A wannan harin dai an yiwa mutane yankan rago, kana an halbe wasu harb lahira, a yayin da aka yiwa mata masu yawa fyade.
Charles Kitambala da matarsa da 'ya'yansu hudu sun yi gudun hijira daga kauyen Ituri, inda ya bayyana abun da ya faru a wancan lokacin;
"A ranar 12 ga watan mayu na shekara ta 2003 ne muka tsere.Muna jin karar harsashen bindigogi da ake harbawa yana shigewa ta kawunanmu. Ana ruwan sama mai tsanani ga matsanancin yunwa".
A baya dai garin na Ituri da ke yankin gabashin Janhzuriyar Demokradiyyar Kongo ya kasance yankin da 'yan tawayen ke fafaftawa. Mayakan tawaye daga kungiyoyi daban daban kan afka wa fararen hula da ke kauyuka, inda kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka yi ta gargadi dangane da irin rayuka dake salwanta. Katambala da iyalinsa dai sun tsallake rijiya da baya kamar yadda ya shaidar;
Ya ce " mun gane wa idanunmu abun da mayakan ke yi, yadda suke yayyaka mutane da wuka. Wannan batu ne da ya zame mawuyaci mu manta har iyakar rayuwarmu."
Katanga da ake yiwa lakabi da sunan "Simba" wanda ke nufin Zaki da harshen Swahili, ya kasance mutun na biyu da aka zartar da hukunci da kafuwar wannan kotu a shekara ta 2002. Tun a watan Disamban shekara ta 2012 kotun ta ICC ta wanke wani madugun 'yan tawaye da aka zargesu tare mai suna Mathieu Ngudjolo. Geraldine Mattioli-Zeltner ta kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta tunatar da yadda shari'ar ta gudana a baya;
" Alal misali sun ce, masu binciken basu samu isa sosai zuwa filin ba. Babu shakka a wasu lokuta akwai batu na tasaro. Amma Alkalan sun nunar da cewar, akwai wasu abubuwan da shaidu suka fada, wadanda ba gaskiya bane, kuma da za'a iya tabbatar dasu da an je filin".
A cewarta dai an samu gibi sosai dangane da binciken, kasancewar kotun ta yi amfani da shaidan da ta samu akan kisan gilla da aka yi a garin Bogoro ne kadai;
" Geraldine ta ce mun yi nadamar ganin cewar, ofishin shigar da kara basu zabi bincike akan kashe kashe da aka yi alal misali a garuruwa uku ba. Da hakan ne zai nunar da cewar akwai mummunan abu daya faru a garin Ituri a shekarata 2003,ta hakan ne da za'a ga irin rawa da mutane biyu da ake zargin suka taka a kungiyoyin tawayensu, wanda zai nunar da irin hare hare da suka kai a kan fararen hula."
Katanga dai yana da 'yancin daukaka kara, kuma zai iya samun hukuncin daurin shekaru 30 a gidan wakafi, idan an gabatar da shari'ar a watanni masu gabatowa.Kontun ta ICC na shan zargin tafiyar hawainiya a gudanar da shari'arta, baya ga suka da take sha na cewar, kararrakin da ake kaiwa gabanta duk na 'yan Afrika ne.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe