ICC ta zargi Boko Haram da aikata laifukan yaƙi
August 6, 2013To an dai daɗe ana samun masu yunƙurin tunkarar kotun ƙasa da ƙasa da ke birnin Hague domin ta bincika abin da ke faruwa a hare-haren da ake kai wa a tsakanin ƙungiyar ta Ahli Sunnah Li Da'awatti Waljihad da martanin da jami'an tsaron Najeriya ke mayar wa, kafin kotun ta ƙasa da ƙasa ta bayana wanan matsayin nata.
Zargin da kotun ƙasa da ƙasa ke yi a kan hare-haren da ƙungiyar ta Ahli Sunnah Li Da'awatti Waljihad ke kai wa a Najeriyar musamman na fararen hula kan cewar ya kai mizanin aikata miyagun laifuffukan yaƙi. Wanda ofishin mai tuhumar aikata miyagun laifuffuka na kotun Fatou Bensouda, ta bayyana cewar bayyanai da suke da su sun nuna alamun hakan abin da ke kama hanyar gudanar da cikakken bincike Barrister Abdulhameed Muhammad ƙwararren lauya ne a fanin dokokin ƙasa da ƙasa don jin illar da ke tattare da hakan.
Nazarin masu yi sharhi a kan wannan al'amari
Ya ce : ‘'Wannan na nuna cewar Najeriyar da al'ummarta sun shiga wani hali kenan a idon duniya saboda irin waɗanan aiyyuka, to amma dai sa'ar da za'a ce Najeriyar na da shi ko kuma wani hanzari shi ne ba ha ka kwai katsam za su shigo ƙasar su gudanar da irin wanan bincike ba. Kuma su waɗanda ake tuhuma ganin suke kamar ba'a ma yi wani hukunci ba, saboda ba wai wata doka ba ce da zata ce ai an kama su an fitar da su Najeriya ko kuma an ɗauki wani mataki. Abubuwan nan yadda suke ta tafiya yana nuna wani hali ne da yanayi da ƙasar ta shiga na maganar ta'addanci''
Hare-haren da ake zargin ƙungiyar na kai wa a kan fararen hula da martanin da jami'an tsaro ke yi tun daga 2009 da yunƙurin kafa gwamnatin islama ya yi dalilin mutuwar mutane fiye da dubu biyu. To ko bayyana cewa sun aikata miyagun laifuffukan yaƙi na iya sauya lamarin ? Malam Abubakar Umar Kari masanin hallayar jama'a ne da ke jami'ar Abuja.
Ya ce ‘'Ba ni tsamani domin ina ganin su magoya bayan wannan ƙungiyar wanan abin baya ma damunsu domin an Don haka ina ganin babu abin da zai canza domin su waɗanan mutane ba su ma amince da wannan tsarin na kotun ba , tasirin da kawai za yi shi ne ya wajen farfaganda kuma mai yiwuwa idan wata rana ƙarfinsu ya ragu aka kama su ana iya gurfanar da su.''
Kotun na zargin ƙungiyar da kashe farar hula
A lokutan baya ƙungiyoyin kare hakin jama'a na Najeriyar da ma ƙasashen duniya sun kasance masu korafin zargin jami'an tsaron Najeriyar da wuce gona da iri suke yi wajen kashe jama'a, a yanzu da kotun ƙasa da ƙasa ba ta yi maganar hukumomin tsaron ba sai na ƙungiyar to ko bayyana wannan mataki da kotun ta yi zai iya sauya yadda wanana ƙalubale ke tafiya a Najeriyar ? Malam Abubakar Umar Kari masanin hallayar jama'a ne da ke jami'ar Abuja.
Ya ce : ''Ni ina ganin wanan fargar jaji ce domin idan har Boko Haram har ta ma aikata wanan laifi, ai kotun yana da wahala ta saka hannu a kansu saboda haka ana ganin Kaman wanan lamarin ne da ke zaman tamkar faɗa amma aikata shi zai yi wuya.''
Duk da kwamitin sulhu da gwamnatin Najeriya ta kafa a ƙokarin shawo kan matsalar har zuwa yanzu lamari na zama wanda ba'a kai ga ganin kama hanyar gano bakin zaren ba, musamman tababar da ke tattare da yunƙurin sulhun kansa .Matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da ƙalubalantar arewacin Najeriya tuni ta yi naso tare da shafar ɗaukacin ƙasar.
Daga ƙasa za ku iya sauraron wannan rahoto haɗe da martanin jma'a a kan batun wanda wakilinmu na Gombe Al-Amin ya aiko mana
Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane