1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC ta saurari jawaban karshe a shari'ar da ake wa Bemba

Mohammad Nasiru AwalNovember 13, 2014

Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ta saurari jawaban karshe a shari'ar da ake wa tsohon madugun 'yan tawayen Kongo.

https://p.dw.com/p/1DmdI
Jean-Pierre Bemba
Hoto: AFP/Getty Images

Shari'ar da ake wa tsohon madugunn 'yan tawayen Kongo Jean-Pierre Bemba Gombo ta kawo karshe a wannan Alhamis bayan da kotun duniya mai hukunta laifukan yaki ta ICC ta saurari jawaban karshe na masu kare wanda ake zargi da aikata laifi. Ana tuhumar Bemba da aikata laifuka biyu a kan bil Adama da kuma laifukan yaki guda uku a kotun ta duniya da ke kasar Netherlands. A lokacin yakin Kongo daga shekarar 1998 zuwa 2003, Bemba ya jagoranci kungiyar Congolese Liberation Movement da Yuganda ta mara wa baya. Ya kwace yanki mai fadi na gabacin Kongon inda ya sayar da lu'ulu'u don samun kudin sayen makaman yaki. Ana kuma zarginsa da kyale dakarun da ke masa biyaya yi wa mata fyade da kwasan ganima a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekareu 2002 da 2003 lokacin da aka tura su can don hana yunkure-yunkuren juyin mulki.