1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC ta bukaci a mika mata Omar al-Bashir

Ramatu Garba Baba
June 19, 2019

Kotun kasa da kasa ta ICC ta nemi a mika mata tsohon Shugaban kasar Sudan Omar Hassane al-Bashir don ya fuskanci shari'a bisa hannu a rikicin da ya lakume rayuka a yankin Darfur.

https://p.dw.com/p/3Kk0P
Sudan Präsident Omar al-Bashir
Hoto: Reuters/M. N. Abdalla

Fatou Bensouda, mai shigar da kara a kotun kotun kasa da kasa ta ICC da ke birnin hague ce ta nemi gwamnatin riko a kasar Sudan da ta mika mata tsohon Shugaban kasar Omar Hassane al-Bashir don fuskantar shari'a,  bisa zargin aikata laifukan yaki a yankin Darfur. Bensouda ta sheda ma Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, a shirye ta ke ta yi aiki tare da mahukuntan Sudan don ganin haka ta cimma ruwa.

Ta ci gaba da cewa yanzu ne lokacin da ya kamata a dauki matakin a kan al-Bashir da sauran wasu mutane hudu da ake zarginsu da hannu a kisan gilla da aka aikata a yayin rikicin na yankin Darfur da ya haifar da matsalar 'yan gudun hijira mafi muni a Sudan, duk kuwa da halin rikici da kasar ke ciki na ja-in-ja a tsakanin masu zanga-zanga da wadanda ke rike da madafun iko. Ita dai kotun ta ICC na son tuhumar al-Bashir ne bisa laifin kisan kiyashi da kuma aikata laifukan yaki a yayin rikicin yankin Darfur na Sudan din.