Husni Mubarak na fama a Asibiti
June 20, 2012Kafafen yada labaru masu zaman kansu a kasar Masar sun ba da rahotannin da ke nuni da cewa tsohon shugaban kasar, Husni Mubarak na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai bayan da ya kamu da ciwon zuciya. Tun da farko kamfanin dillacin labarun gwamnatin kasar wato MENA ya sanar da mutuwar tsohon shugaban. To ama sai majalisar koli ta sojin kasar ta karyata hakan. A jiya talata ne dai ake dauki Mubarak zuwa wani asibitin soji bayan da ya kamu da ciwon hawan jini.
A farkon shekarar 2011 ne Mubarak ya yi murabus daga matsayinsa na shugaban kasar bayan da jama'a suka shafe makonni suna gudanar da zanga -angar nuna adawa da gwamnatinsa. Shi dai tsohon shugaban da ya shafe shekaru kusan 30 yana jan ragamar kasar a farkon watan Yuni kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa laifin kashe mutane sama da dari 800 da suka shiga zanga-zanga nuna adawa da shi a shekarar 2011 .
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu