Hukuncin kotu kan harin filin jirgin saman Frankfurt.
February 10, 2012Talla
Wata kotu a jihar Hesse dake nan Jamus ta zartar da hukuncin ɗaurin rai da rai akan wani mai tsatsauran kishin Islama wanda ya hallaka sojojin Amirka biyu a yayin wani hari a filin jirgin saman Frankfurt a shekarar bara. A ƙarƙashin dokokin Jamus ba za'a yi masa afuwa ba har sai bayan ya yi aƙalla shekaru 15 a gidan yari. Kotun ta sami mutumin mai shekaru 22 da haihuwa da laifuka da dama waɗanda suka haɗa da aikata kisan kai da kuma jikata wasu sojojin guda biyu. Masu gabatar da ƙara sun ce mutumin ɗan ƙabilar Albaniya, haifaffen Kosovo ya girma ne a nan Jamus amma kuma ya zama mai matsanancin ra'ayi wanda ke son taimakawa Jihadin Islama.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi