Hukunci kisa kan masu fyade a Indiya
April 4, 2014Mai gabatar da kara Ujjwal Nikam ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewar ya roki kotun da ta zartar da hukuncin kisa kan mutanen bisa ga shaidun da ya gabatarwa kotu da ma dai amincewa da aikata laifin da mutanen suka yi.
A cikin watan da ya gabata ne dai mutanen suka amince da wannan laifi da suka aikata cikin wata tsohuwar masaka a birnin na Mumbai lokacin da matar ke gudanar da aikinta na daukar hoto.
Indiya dai ta bijiro da hukunce-hukunce masu tsauri kan wanda suka aikata laifuka na fyade bayan da al'ummar kasar suka gudanar da bore cikin shekarar 2012, lokacin da wasu gungun karti suka yi wa wata daliba mai koyon aikin likita fyade da kuma yi mata rauni, wanda yai sanadiyyar rasuwarta.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar