1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ICC kan saka yara a aikin soja

Salissou Boukari
October 11, 2016

Kotun kasa da kasa ta ICC ko CPI za ta soma wani zama domin duba hanyoyin biyan diyya wanda shi ne irinsa na farko ga yara matasan da aka yi amfani da su a matsayin sojojin yaki a Kwango.

https://p.dw.com/p/2R6HZ
Internationaler Strafgerichtshof in Den Haag ICC
Hoto: AP

Wannan zama na kotun ta ICC da zai ci gaba har ya zuwa ranar Alhamis, zai bai wa alkallan kotun damar sanin irin adadin kudadan da ta kamata a bai wa ko wane daya daga cikin yaran da aka yi amfani da su a matsayin sojoji, wadanda madugun 'yan tawaye na wancan lokaci Thomas Lubanga ya saka su ciki a shekara ta 2002 da 2003.

A kalla dai an ware kudi kimanin miliyan daya na Euro kan wannan batu daga cikin asusu na musamman da aka tanada kan iri-irin wannan matsala kamar yadda yarjejeniyar birnin Roma wadda ta tanadi kirkiro da wannan kotun ta kasa da kasa ta ICC ta tsara.

A shekara ta 2015 alkallan kotun sun amince cewa Thomas Lubanga da aka yanke wa hukunci a shekara ta 2012, shi ne zai biya diyyar wadan nan yara da ya dauka a matsayin sojojin yaki, inda kawo yanzu da dama daga cikinsu ke fuskantar wariya da tsangwama daga al'umma.