Hukumomi a Nijar sun cafke Hama Amadou
November 15, 2015Talla
Hama Amadu dai da ke kasancewa tsohon shugaban majalisar dokokin Niger na daga cikin fasinjojin da suka sauka cikin jirgin sama mallakar kamfanin sufurin jiragen sama na Faransa wato Air France a filin saukar jiragen sama na Djori Hamani.
Rahotanin na cewar jami'an tsaro sun datse hanyoyin zuwa filin saukar jiragen sama inda gabanin zuwan sa aka sha artabu tsakanin 'yan sanda da magoya bayansa. Bayan saukarsa dai hukumonin tsaron kasar sun kama shi inda suka ize keyarsa zuwa kurkuku.
Shugaban na jam'iyyar Lumana ya fice daga Nijar ne a shekara ta 2014 zuwa Faransa bayan da kotu ta tuhumeshi da laifin yin safara jarira da shi da maidakinsa.