Covid-19 ta sa Holland ta rufe iyaka da Birtaniya
December 20, 2020Talla
Gwamnatin Holland ta soke duk wani saukar jiragen sama a kasar daga Biraniya a wani mataki na kare kanta, biyo bayan samun wani nau'in kwayar cutar Covid-19 da ya bayyana a wani bangare na kasar Birtaniya.
Matakin da tuni ya soma aiki zai shafe tsawon kwanaki 10 ne, a cewar wata sanarwar da hukumomin kasar ta Holland suka bayyana.
Wannan lamarin na zuwa a daidai lokacin da jami'ai a Birtaniya, suka dauki dokar kulle a birnin Landan da yankin Kudu maso gabashin kasar bisa bullar cutar da aka hakikance mai saurin yaduwa ga jama'a.