An kama maharin birnin Utrecht
March 18, 2019Talla
Mutumin nan da ake zargi da kisan mutane uku a birnin Utrecht na kasar Holland ya fada komar 'yan sanda kamar yadda jami'an suka bayyana a yammacin wannan Litinin.
'Yan sandan dai sun yi nasara ta kama Gokmen Tanis dan shekaru 37 haifaffen Turkiyya bayan daukar sa'oi masu yawa suna nema biyo bayan harin da ake zargin sa da kaiwa a tashar jirgin kasaa birnin na Utrecht.
Magajin gari Jan van Zanen ya fitar da wani sako na bidiyo inda ya ce mutane uku sun halaka kuma akwai mutane biyar da suka samu raunika a harin sabanin mutane tara da ake fadi tun da fari.