Dan majalisar dattijai mai wakiltar jihar Kano ta tsakiya, Sanata Rufai Sani Hanga, ya ce za su yi gyara kan doka da zai hana gwamnoni karya dimukuradiyya a zaben kananan hukumomi a Najeriya. Sanatan ya kuma yi karin haske kan halin da kasa ke ciki da kuma batun cewa yana jin yunwa shi ma.