1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashiya mai sana'ar Carbin Malam

April 8, 2020

Wata matashiya a jihar Katsina da ke Najeriya ta kama sana'ar wata alawa da ake kira da Carbin Malam domin dogaro da kanta. Matashiyar ta ce ta samu nasarori kuma yanzu haka ta mallaki abubuwa da dama na rufin asiriri.

https://p.dw.com/p/3aaSA
Eine Schüssel mit Bonbons
Hoto: Fotolia/tanjichica

Wannan matashiya mai suna Basira Hamza tana aure a garin Charanci da ke jihar ta Katsina a Najeriya. Matashiyar na daya daga cikin matan da ba su yarda da zama ba sana'a ba, da ma kuma masu iya magana kance duk mai jiran wani ya wahala. Hakan ce ta sanya ta taimakawa kanta ta rungumi wannan sana'a domin dogaro da kanta.

Acewarta hakarta ta cimma ruwa sakamakon wannan sana'a ta Carbin Malam, ta la'akari da nasarorin da ta samu, ta ce mai gidanta ma ya shaida hakan, domin kuwa, tana dauke masa wasu hidindumu na yau da gobe a cikin gidan, domin a gudu tare a tsira tare. Matashiya Basira ta ce ta dandana kudarta a baya, saboda zaman jiran Allah baku mu samu da ta yi kafin ta fara sana'a. Basira ta ce tana amfani da sikari da kwakwa da dan tsami wajen hada alawar ta Carbin Malam, kuma yara da manya na sha.