Matashiya mai sana'ar kira a Katsina
November 25, 2020Talla
Matashiyar mai suna Hadiza Sani da ke sana'ar kira a Katsina, ta kafa kayan kirar ne a Kofar gidan mahaifinta. Hadiza ta ce ita kam sana'ar kira sai godiya, kasancewar ta cimma manufar da ta sanya ta rungumeta, ta la'akari da irin nasarar da ta yi.
Sai dai a bangare guda wannan matashiya da ke sana'ar kira a jihar ta Katsina, ta ce bayan nasarorin da ta cimma akwai kuma kalubale. Kira dai sana'a ce da ba ta yiwuwa mutum daya, abin da yasa Amina Sani take kamawa wannan matashiya wajan wana injin da ke ba ta wuta, yayin da take kera ka yayyakin.