Sayar da kaya ta kafafen sada zumunta
February 3, 2021Matashi mai suna Abdoulrazak Hima Sido da ke da shekaru 27 a duniya, ya kama wannan sana'ar ne bayan da kammala karatunsa na digiri, inda ya karanci fannin aikin hukuma. Ya kuma bayyana cewa, tun yana yaro sana'o'i ke birge shi kasancewar ya tasao gidansu ana yin sana'o'i. Ya kara da cewa ya fara sana'ar ne bayan da ya ga wata mata ta saka kayayyakin a shafinta na Facebook tana tallansu.
Abdoulrazak ya bayyana cewa daga lokacin da ya dauki lambar matar suka yi magana ne sai ta fara turo maa da kayan inda shi ma yake dorawa a kafafensa na sada zumunta. Ya kara da cewa kwalliya ta biya kudin sabulu da wannan sana'a tasa. Sai dai Abdoulrazak ya nunar da cewa, duk da nasarorun da ya samu akwai kalubale, inda babbar matsalar ita ce ta rashin karfin internet da kuma yadda wasu kan ce suna son kaya ya ajiye musu, daga bisani kuma suce sun fasa.