Tattalin arziki
HdM: Mai lalurar kafa na hada takalma
October 13, 2021Talla
Matashin Murtala Abba Galidima wanda ba ya iya tafiya sai dai jan gindi, yana sana'ar hada takalma ne a cikinbBirnin Katsina. A cewarsa da ya rika bara gara ya kama sana'ar domin tsira da mutuncinsa. Murtala ya koyi sana'ar ne, inda daga bisani shi ma ya bude wurinsa. Ya ce dalilin sana'ar ya samu nasarori sosai kuma yana samun ciniki, koda yake Murtala ya ce ba a rasa tarin kalubale. Burin Murtala dai shi ne, ya samar da babbar masana'antar hada takalma domin tallafa wa matasa su samu aikin da za su dogara da kansu.