Ko rikicin Gabas ta Tsakiya zai zo karshe?
November 27, 2024Shugaban Amurka Baiden da kasarsa ta kai gwauro ta kai mari domin kawo karshen yakin, ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar da ya ce yana fatan za ta zama danbar cimma makamanciyarta a Gaza. A sabon tsarin yarjejeniyar sojojin Isra'ila za su janye daga Lebanon, kana dakarun Hezbollah za su janye daga kudancin Kogin Litani da ke kusan kilomita 30 daga iyakar Isra'ila da kasarsu a maye gurbinsu da sojojin Lebanon da za su dauki alhakin saye da kera duk wani makami a kasar. Amurka ce za ta jagoranci kwamitin kasashe biyar, wadanda za su sanya ido a tsagaita wutar da tabbatar da an mutunta ta. Tuni dai firaministan Isra'ila Benjamin Netanjahu ya yi alkawarin mutunta yarjejeniyar, bayan taro da ya yi da majalisar kolin tsaron Isra'ila da kuma samun lamunin majalisar dokoki. Tuni dai shugaban 'yan adawar Isra'ila Yair Lapid ya soki gwamnatin Natenyahu kan kin cimma yarjejeniyar, inda ya ce in har za a iya cimma wannan matsaya cikin watanni uku da fara yaki da Hezbollah bai ga dalilin kin cimma makamanciyarta a Gaza ba. Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Kasashen Larabawa da ta Tarayyar Turai sun yi farin ciki da cimma yarjejeniyar, suna nuna muhimmancin gaggauta shigar da kayan agaji da fara gyara ababen jin dadin rayuwar jama'a a kasar ta Lebanon.