Mace mai sana'ar kuli-kuli Katsina
April 29, 2020Matashiyar mai suna Hauwa'u Lawal dai na zama a bakin tashar kofar Marusa cikin birnin Katsina, inda take sayar da kuli-kulin, kuma ta ce gajiya ta yi da takurawa iyayenta da bani-bani ta saukaka musu ta kama wannan sana'ar. Akwai tarin kalubale da wannan matshiya ta ce ta fuskanta a baya a wannan sana'ar, amma kuma bai sanyaya mata gwiwa ba, a cewarta juriyar da ta yi ce ta sanya har aka samu mafita, sai dai har yanzu akwai kalubalen da ba a rasa ba.
Matashiya Hauwa'u dai ta bayyana cewa ta kammala karatunta na sakandire kuma tana da fatan ci gaba da karatun, amma duk da haka ta ga babu abin da ya kamace ta illa ta zamo mai dogaro dai kanata. A kasar Hausa akwai al'adar raina sana'a musamman tsakanin matasa, abin da ya sanya Hajiya Yalwati Bature Abdullahi ta shawarci Hauwa'u da ta kawar da kanta daga masu irin wannan dabi'ar.
Sakamakon yadda wannan matashiya Hauwa'u ta kama wannan sana'a domin tsira da mutunci ya sanya ta zama abar kwatance a cikin kawaye kuma abar alfahari ga iyayenta saboda irin gudummuwar da take ba su.