Harin 'yan tawayen Mao a Indiya ya hallaka 24
May 26, 2013'Yan sanda a Indiya sun ce 'yan tawayen Mao wajen su 300 waɗanda kuma suka yi ɗammara da manyan makamai sun hallaka aƙalla mutane 24 bayan da suka kai hari kan wani ayarin motocin da ke ɗauke da shugabanni da magoya bayan Jamiyyar Congress a matakin ƙaramar hukuma, a ɗaya daga cikin jihohin da ke tsakiyar Indiya.
Wannan harin shine mafi muni a tsukin shekaru uku, kuma na baya-bayan nan a taƙaddamar da ke tsakanin ƙungiyar tawayen da hukumomin ƙasar.
Shugabar Jamiyyar Sonia Gandhi wadda ta ruga Jihar da wannan bala'in ya afku tare da shugaban ƙasa Mahmohan Singh sun yi allah wadai da harin, wanda aka ce wasu 37 sun yi mummunar rauni kuma suna karɓar magunguna a asibiti.
Ga dai shaidar da wani wanda ya ganewa idanunsa yadda wannan hari ya afku ya bayar
"'Yan tawayen sun tsayar da mu suka fara kai mana hari, sai shugaban jamiyyar mu ya sauko daga na sa motar ya roƙe su ya ce kada su kashe kowa banda shi, sai suka harbe shi da harsasai sun kai ɗari sanan daga ƙarshe suka harbe shi da dutse a goshi"
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman