Harin ta'addanci a Nairobi ya daukii hankalin Jaridun Jamus.
January 18, 2019Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce a ranar Talatar nan ce kotun sauraron manyan laifuka ta ICC ta wanke tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo akan tuhumar rikicin bayan zabe da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3000 a 2010 da 2011. Jaridar ta cigaba da cewar, a shekara ta 2011 ne dai aka zartar da shari'ar dauri a kan Gbagbo saboda samunsa da laifin cin zarafin al'umma.
Ya kasance shugaban wannan kasa da ke yankin yammacin Afirka daga shekarata 2000 zuwa 2005. A shekara ta 2002 rikicin mayakan sa kai ya raba kasar gida biyu, Arewaci da Kudanci. Gbagbo ya ki barin gwamnati a karshen wa'adin mulkinsa a 2010, duk da cewar ya fadi zabe.
Da tallafin sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya aka cafke Gbagbo tare da mika shi gaban kotun shari'ar manyan laifuka ta ICC da ke Hague, daga bisani aka rantsar da wanda ya gaje shi Alassane Ouattara, da ya sake samun nasarar zarcewa a zaben shekara ta 2015.
Ta'addanci ya sake komowa
Jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta labari mai taken " Ta'addanci ya sake komowa". Jaridar ta ce wajen mutane 20 ne suka rasa rayukansu a harin da kungiyar al-Shabaab ta yi ikirarin kaiwa a wani fitaccen otel da baki 'yan kasashen waje suka fi sauka. Daruruwan mutane ne dai aka kubutar da su daga harabar ginin, a lokacin da maharan ke cigaba da bude wuta. Nan take mutane 14 aka tabbatar da sun mutu ciki har da wani Ba Amurke da kuma dan kasar Birtaniya, a yayin da mafi yawa 'yan asalin kasar Kenya ne, daura da wadanda suka jikkata, inda daga bisani yawan wadanda harin ya ritsa da su ya kai wajen mutum 20.
Bunkasar Noman Shinkafa a Najeriya
Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce godiya ga horoswa kan tsarin noma na zamani wanda ya haifar da kyakkyawar sakamako.Jaridar ta cigaba da cewar, amfani da tsarin noman shinkafa na zamani a bangaren manoma a Najeriya, ya taimaka wajen bunkasar shinkafa a daidai lokacin da mabukatu ke karuwa.
Karuwar masu amfani da shinkafa a nahiyar Afirka dai wata babbar dama ce ga kananan manoma. Wani shiri na bayar da tallafi ga manoman ya nunar da yadda karamin taimakon kudi, zai iya yin tasiri wajen habaka noman shinkafa. A kasashen Afirka, Kudu da Sahara a 'yan shekarun da suka gabata, an samu karuwar masu cin shinkafa da wajen kashi uku daga cikin 100, nau'in abincin da a baya sai gidan masu hannu da shuni ake gani. Saboda karuwar mabukatu, kananan manoma na fuskantar matsalar samar da adadin da ake nema. Batun da ake gani a zahiri a kasa kamar Najeriya da ta fi kowace kasa yawan al'umma a nahiyar Afirka, da yawan mutane wajen miliyan 190.