1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake kusa da asibiti a Maiduguri

Mohammad Nasiru AwalJuly 1, 2015

Harin da ya auku dab da wani asibiti mai nisan kilomita 10 daga Maiduguri ya zo ne daidai lokacin ziyarar matamakin shugaban Najeriya a birnin.

https://p.dw.com/p/1FrOS
Nigeria Selbstmordanschlag auf Markt in Maiduguri
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Jossy Ola

Wasu 'yan harin kunar bakin wake su biyu sun tarwatsa kansu a kusa da wani asibiti da ke Maiduguri Arewa maso Gabashin Najeriya, jim kadan bayan mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya isa birnin a wata ziyarar ba zata a sansanonin 'yan gudun hijirar da ke tsere wa rikicin Boko Haram. Harin da ya auku kusa da kofar asibitin na kauyen Molai mai tazarar kilomita 10 daga birnin Maiduguri ya kuma raunata mutum biyu. A ranar Asabar 'yan kunar bakin wake sun hallaka mutane uku sannan sun raunata 16 a wani hari da suka kai a wannan asibiti. Rahotanni sun ce wata matashiya da wani matashi suka kai harin na wannan Laraba. Yemi Osinbajo na ziyarar wani sansanin 'yan gudun hijira mai tazarar kilomita 10 daga wurin da aka kai harin.