1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Boko Haram a wasu garuruwan Borno

August 18, 2014

Wasu mutane fiye da goma a kan babura sun kai hari a garin Durwa da Maforo da ke jihar Borno, inda suka kashe 'yan asalin garin da dama..

https://p.dw.com/p/1Cwbg
Hoto: AFP/Getty Images

A ranar 6 ga watan Yuli da ya gabata ne yan bindigar suka kai hari a garin na Krenuwa, inda suka kashe mafi yawan mutanen garin tare da kokkona gidaje da ma ofishin 'yan sanda da sansanin soje dake garin. Sai dai a wannan karon 'yan bindigar da suka iso garuruwan na Durwa da Maforo, sun zo ne bisa babura.

Sun tattara mutanan garin, sannan daga bisani suka fidda 'yan asalin garin Krenuwa dake zaune a wadannan garuruwa, inda suka kashe mutane 10 daga cikinsu. Sannan kuma an harbe, shid , yayin da hudu kuma suka yankasu gunduwa-gunduwa, a cewar wani dan garin na Durwa da ya gane wa idanunsa.A halin yanzu shi ma ya gudu ya zuwa Maiduguri.

Wannan harin dai ya kasance wani mataki, na mayar da martani ga sojin kasar ta Najeriya da suka kai wa 'yan kungiyar ta Boko Haram hari bayan harin na Krenuwa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe