1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Boko Haram a garuruwan Jihar Borno

Salissou BoukariFebruary 13, 2015

Mutane 21 suka rasu sakamakon wasu hare-hare da 'yan Boko Haram suka kai a garuruwan Akida da Mbuta da ke cikin jihar Borno a arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1EbNW
Hoto: AFP/Getty Images

A cewar wata majiya ta hukumomin yankin da kuma wadanda suka ganewa idanunsu wannan lamari, a garin Akidai da ke a nisan km 25 da birnin Maiduguri 'yan kungiyar sun hallaka mutane 12, sannan suka hallaka wasu guda tara a garin Mbuta a wani hari da suka kai a ranar Alhamis da ta gabata, majiyoyin sun tabbatarwa kanfanin dillancin labaran Faransa cewa, maharan sun kuma kona gidaje da shaguna.

Da sanyin safiyar wannan Jumma'a ce kuma 'yan kungiyar ta Boko Haram suka kai harinsu na farko a wani gari da ke kasar Cadi inda suka kashe a kalla mutane biyar kusa da wani sansanin 'yan gudun hijira a cewar Kanar Azem Bermandoa Agouna kakakin sojan kasar ta Cadi.