Harin bam a wata makarata da ke Zariya
September 30, 2012Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin Yusha'u Shu'aibu, jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta NEMa da ke Kaduna ya ce harin har wa yau ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama.
Bam ɗin da ya tashi da harbe-harben sun faru ne a kusa da wata makaratar kwana ta addinin Islama mallakin sananen malamin addinin Islaman nan na Zariya Awwal Adam Albani.
Shaidun gani da ido sun bayyanawa manema labari cewar tashin bam ɗin ya yi sanadiyyar lalacewar wani bangare na makarnatar da kuma wasu gidaje da kusa da ita.
Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗau alhakin kai harin. Harin dai na zuwa ne kwana guda kafin bikin ranar zagayowar cikar Najeriya shekaru hamsin da biyu da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya, bikin da mahukuntan ƙasar su ka ce ƙwarya-ƙwarya za a yi lamarin da ya sa dama ke ganin cewa hakan na da nasaba da ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman