Harin ban ya kashe mutum 35 a Somaliya
January 4, 2023Talla
Wannan dai shi ne harin baya-bayan nan da kungiyar ta al-Shabaab mai alaka da al Qaeda ta kaddamar, tun bayan da dakarun gwamnati da na mayakan kawancen hauloli, suka fara fatattakar tsagerun daga yankunan da suka dade suna rike da su.
Abdullahi Osman da ke zama daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen aikin ceto bayan mummunan harin, ya ce akwai wasu gommai da suka jikkata, wasu sun yi muni.
Tuni kafar yada labaran kungiyar ta al-Shabaab, a cikin wata sanarwar ta dauki alhakin harin.