Hari a kan wata kasuwa a Maiduguri
September 20, 2014Talla
Maharan sun kashe aƙalla mutane 36, kana Wasu majiyoyi har guda biyu na jami'an tsaro, sun tabbatar da cewar an ci gaba da kai harin tun daga jiya Jumma'a har yazuwa yau Asabar.
Maharan sun shiga kasuwar ne, sanye da kayan sojoji da na 'yan sandar Najeriya, inda suka harba roka, kafin su ci gaba da buɗe wuta. A cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai fararan hulla aƙalla 23, kuma rahotanni sun ce maharan sun kwashi kayayyakin abinci da suka loda kan manyan motocin da 'yan kasuwar suka gudu suka bari.