1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari a kan jami'an kwastom a Katsina

March 16, 2014

wasu mutane dauke da bindigogi ne suka kai harin a Jibiya da ke kan iyakar Najeriya da Nijar. Wata majiya ta ce an yi asarar rai, lamarin da babban jami'in kwastom ya karyata..

https://p.dw.com/p/1BQWa
Hare-hare sun zama ruwan dare a arewacin NajeriyaHoto: AMINU ABUBAKAR/AFP/Getty Images

Kakakin hukumar kwastom na jihar katsina ya shaida wa wakilinmu na wannan jiha cewar wasu mutane biyu dauke da bindigo cikin wata mota kirar J5 suka kai wannan harin. Jami'in ya kuma kara da cewa ma'aikatan da aka harba na asibiti inda suke karbar magani. Sai dai kuma an sallami daya daga cikinsu daga asibiti.

Yanzu haka ana gudanar da bincike domin tantance wadanda suka kai wannan hari a Katsina. Babban jami'in kwastom na wannan jiha ya ce babu wanda aka kashe. Amma wasu majiyoyi suka ce tabbas akwai mace-mace. Kwanaki ukun da suka gabata ne dai wasu 'yan bindiga a kan babura, suka halaka mutane fiye da 100 a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa da Safana a jihar ta Katsina.

Mawallafi: Babangida Jibril/USU
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe