Somaliya: Harin bam ya ritsa da sojoji
June 15, 2024Talla
Fashewarbam din ya faru ne a lokacin wani sintiri a kusa da garin Gofgaduud mai tazarar kilomita 30 daga garin Baidoa da ke a kudu maso yammacin kasar. Sama da shekaru 16 kenan masu kishin Islama ke yakar gwamnatin Somaliya Ko da yake a shekarar ta 2011 dakarun Tarayyar Afirka sun fatattakesu daga babban birnin kasar, amma har yanzu suna a yankunan karkara na somaliyar.