Hanyoyin tabbatar da tsaro a tashoshin haƙar man fetur
August 28, 2012Rundunar tsaro ta gamayya wato JTF da ke yankin Nigerr Delta,ƙarƙashin rundunar askarawan Najeriya shiyya ta 82,ta buɗe taron yini huɗu don duba irin rawar da rundunar ta JTF ke takawa a aikin tsaron harabobin ayyukan mai a yankin Niger Delta,da kuma ta sauran masu ruwa da tsaki a harkar.Irin wannan taro dai kan gudana duk shekara,sai dai taron na bana ya maida hankali kacokan kan matsalar satar ɗanyen mai.
Rundunar gamayyar tsaro ta JTF da ke yankin na Niger Delta da suka haɗa da jami' an soji,da 'yan sanda,da EFCC da kuma na jami'an hukumar sifiri ta ruwa wato NIMASA,aikinsu ne su tabbatar da tsaro a harabobin da kamfanonin mai ke aikin lalubowa tare da haƙo ɗanyen mai,da kuma a yau ba a gobe ba ,Najeriya ta dogara kusan kacokan kai,a matsayin hanya ta shigowar kuɗaɗe.
Wannan taro da kan gudana duk shekara,taron na bana ya maida hankula kacokan kan yadda satar ɗanyen mai tare da dafa shi ta bayan fage ke ƙara zama ƙalubale ga gwamnatin Najeriya,da kamfanonin mai,gami kuma ga tattalin arzikin ƙasar.Akwai dai ƙasidu da aka shirya gabatarwa a iya kwanaki biyar da rundunar ta JTF ta keɓe don taron.Birgediya Janar T.Y. Burutai shine jagoran taron,kuma ya gabatar da ƙasida kan rawar da ma su ruwa da tsaki a harkokin mai za su iya takawa domin shawo kan matsalar ta satar ɗanyen mai.Br Janar Burutai yace muna sane da fahimtar jama'a na cewar jami'an tsaro na tsoma kansu cikin badaƙƙalar cin hanci a aikinsu na tsaro a yankin,to amma dai a tsaye muke wajen maganin hakan,sannan kuma ya zama wajibi a yiwa harkar shari'a garambawul bisa la'akari da yadda ma su aikata laifin satar mai ke sha bayan miƙa su ga shari'a.
A taron dai, an nunar cewar manyan dalilai da ke assasa halayyar satar ɗanyen mai da matasa ke yi a yankin Niger Delta sun haɗa da rashin ayyukan yi ga matasan,da rashin haɗin kan shugabannin al'ummomi da kuma wasu kamfanonin mai don tunkarar matsalar,sannan da yadda kamfanonin mai gami da NNPC mallakin gwamnatin tarayya sukai watsi da layukan payip payip ɗinsu ba tare da bin kadinsu ba akai akai,haka kuma an nunar da sarƙaƙƙiyar da ke akwai a hanyoyin ruwaye don aikin tsaro ɗin,da kuma ke bukatar ƙaddamar da sabbin dabaru na tsaro ma su cike da fasahar zamani.
Biliyoyin daloli ne dai Najeriya ke hassara a duk shekara a sakamakon ƙazantar satar danyen mai a yankin na Niger Delta.
Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Yahouza Sadissou Madobi