Ganawa tsakanin jagororin rikicin Sudan ta Kudu
June 22, 2018Jagoran 'yan tawaye kana tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar ya amince da tafiya birnin Khartoum na Sudan domin ganawa da babban mai adawa da shi Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu.
Mai magana da yawun Machar ya tabbatar da labarin ganawar zagaye na biyu bayan mutunen biyu sun tattauna a birnin Addis Ababa na Habasha kan hanyoyin shawo kan rikicin na Sudan ta Kudu.
Wannan ganawa da aka yi a birnin Addis Ababa ta zama ta farko tsakanin Shugaba Kiir da tsohon mataimakinsa Machar cikin shekaru biyu da suka gabata, kuma rikicin da ke faruwa ya jefa milyoyin 'yan Sudan ta Kudu cikin hukuba. Tun shekara ta 2013 kasar ta fada cikin rikicin lokacin da Shugaba Salva Kiir ya fatattaki tsohon mataimakinsa Riek Machar daga bakin aiki.