1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Hana koyar da darussan jima'i

Gazali Abdou Tasawa LM
November 28, 2024

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bayar da umarnin dakatar da koyar da wasu darussa a makarantun firamaren kasar, wadanda ta ce sun saba wa al'adu.

https://p.dw.com/p/4nXX6
Jamhuriyar Nijar | Makarantun Firamare | Ilimin Jima'i | Haramtawa
Matakin hana koyar da darussan da ke da nasaba da jima'i a Jamhuriyar NijarHoto: picture alliance / ZB

Wasika ce mai karfin doka ministar ilimi ta rubuta ta aike wa hukumomin ilimi a fadin Jamhuriyar Nijar, tare da umartar su kan dakatar da koyar da wasu darussa guda bakwai a makarantun firamare da wasu darussan 11 a makarantun CEG wato kanana makarantun sakandare na kasa. Ma'aikatar ilimin ta Nijar din ta ce darussan sun sabawa al'adu da addinan kasar, kuma za su iya yin tasiri wajen gurbata tarbiyyar yara 'yan makaranta tun suna kanana.  da ake koyar wa yara 'yan firamare sun sabawa al'adun Nijar. Kuma ma'aikatar ilimin ta ce ta dauki matakin ne sakamakon korafin da wasu iyayen yara 'yan firamare suka yi kan wadannan darussa da suka hadar da na sanin al'aura da tsarin halittar jikin dan Adam a lokacin balaga da batun da ya shafi jima'i da suke zargin na koyar da batsa ga yara da kuma ka iya lalata musu tarbiya.

Nijar: Matsalar tsaro ta shafi ilimi

Tuni dai kungiyoyin da ke fafutukar kare martabar ilimi a Nijar suka soma bayyana gamsuwarsu da wannan mataki, kana wasu malaman makarantun na ganin baya ga matakin gwamnati na dakatar da darussan masu maganar batsa akwai bukatar iyayen yara su bayar da hadin kai ga shirin ta hanyar daukar mataki na musamman kan yaran nasu a cikin gida. Yanzu haka dai gwamnatin ta Nijar ta sanar da shirin kafa wani babban kwamitin malamai da sauran masana ilimin koyarwa da na tarbiyya, domin binciken illahirin darussan da ake koyarwa a makarantun firamare da na sakandare a kasar da nufin tsarkake su daga duk wasu darussa da ka iya lalata tarbiya ko tayar da hankali a cikin kasa.