Hama Amadou ya tsere daga Nijar
August 28, 2014Talla
A cewar wakilinmu Gazali Abdou Tasawa, kafofin yada labarai na radiyo da talabijin mallakar gwamnatin kasar ne suka tabbatar da wannan labari a daran jiya Laraba, ba tare da wani karin bayani ba. Dama dai tun a jiya kwamitin gudanarwa na majalisar dokokin kasar, ya baiwa gwamnatin kasar izinin mika shugaban majalisar dokokin a kotu, domin ya bayar da bahasi akan zargin da ake yi masa na kasancewa da hannu a badakalar cinikin jarirai.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu