Hama Amadou ya ce gwamnatin Nijar ta yi masa ƙazafi
July 22, 2014Tun lokacin da jam'iyyar ta Hama Amadou ta Modem Luman Afrika ta fice daga ƙawance jamm'iyyun siyasar masu mulki aka fara kai ruwa rana tsakanin ɓangarorin biyu.
Hulɗa tsakanin sassan biyu ta ƙara dagulewa a baya-baya nan
Dangantaka tsakanin jam'iyyar ta Lumana Afrika da jam'iyyar da ke yin mulki ta ƙara dagulewa, biyo bayan wasu hare-haren da aka kai a gidan matamakin shugaban majalisar na huɗu, da kuma cibiyar jam'iyyar PNDS,Tarayya abin da ya janyo aka tsare wasu magoya bayan jam'iyyar Lumana.
Kafin daga bisanin a bangaɗo wannan lamari na cinikin jarirrai wanda a cikinsa aka cafke mutane 21 waɗanda suka haɗa da maiɗakin shugaban majalisar dokokin.
Hama Amadou ya ƙaryata cewar matarsa na da hannu a cikin lamarin
A lokacin wani taron manema labarai da ya yi shugaban majalisar ya bayyana cewar shugabannin na neman shafa masa kashin kaji ne.
'' Wannan batu na fataucin jarirrai har kawo yanzu babu wasu hujjojin da su ka tabbatar da shi kuma da gaskiyya ne sai su bayyana hujjojin.''
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto
Mawallafi : Gazali Abdou Tassawa
Edita : Abdourahamane Hassane