1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hama Amadou na zargi ga taka dokoki a Nijar

October 24, 2014

Shugaban Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar Hama Amadou dake ci gaba da zaman gudun hijira a Faransa, ya zargi hukumomin kasar ta Nijar da taka dokokin kasa.

https://p.dw.com/p/1Dbur
Hama Amadou
Hoto: DW/S. Boukari

Tun bayan da aka zarge shi da hannu cikin batun safarar jarirrai, shugaban Majalisar dokokin ya zargi hukumomin kasar ta Nijar da laifin kulla masa makalkashiya don kawai su hanashi tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2016, inda daga inda yake gudun hijirar, Hama Amadou ke ci gaba da zargin hukumomin na Nijar da laifin almubuzranci da dukiyar kasa inda a cikin fira da yayi da sashen Faransanci na DW yake cewa: Dimokradiyar Nijar na cikin hadari, 'yan Nijar sun yi kokowa don kasar ta samu dimokradiya mai inganci, amma yanzu sabanin haka yan kasar ta Nijar na cikin ukuba, domin mutane ne da basu san mine dokokin kasa ba, minene kundin tsarin mulkin kasa ba, suke mulki, kuma suke tsammanin ta hanyar amfani da karfi ne zasu mulki kasar ta Nijar

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba