1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Ghana: Hakar ma'adinai ba kan ka'ida ba

Ngutjinazo, Okeri AMA/ LM
October 3, 2024

Hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a kasashen Afirka na ci gaba da gurbata muhalli da kuma yin illa ga lafiyar al'umma musamman ma jarirai tun suna ciki, sakamakon shakar sinadarai da iyayensu mata ke yi.

https://p.dw.com/p/4lNIt
Afirka | Illa | Hakar Ma'adinai | Haramtacciyar Hanya | Ghana | Afirka ta Kudu | Najeriya
Hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, na neman zama ruwan dare a AfirkaHoto: DW

Wannan lamari ya janyo zanga-zanga daga masu fafutukar kare muhalli a kasar Ghana, wadda ke cikin sahun gaba cikin kasashen Afirka da ke fama da matsalar ta hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba. JAmi'an tsaro sun cafke masu zanga-zangar da dama, bayan arangamar da suka yi. Gwamnatin Ghana ta jima tana fuskantar matsin lambar kawo karshen aikin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da aka fi sani da galamsey, wanda ta sha nanata alkawarin magance wa. Da hadin kan wasu 'yan kasashen waje da kuma gurbatattun 'yan siyasar Ghana, lamarin na galamsey a Ghana na lalata yankunan karkara da ke da arzikin na al'barkatun kasa da ake hakowa. Daga cikin illolin da wannan matsala ke haifarwa akwai rashin samun tsaftataccen ruwa da sinadaran mercury da na cyanide ke kwaranya a ciki, sai lalacewar kayan amfanin gona da ma kasar noman dungurungun sakamakon zaizayewar da take baya ga lalacewar gandun daji.

Afirka: Hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba

Tun bayan da ya karbi rantsuwar kama shugabancin Ghana, Shugaba Nana Akufo-Addo ya sha alwashin kawo karshen wannan mummunar sana'a da har yanzu alamu ke nuni da cewa abin ya gagari kundila. Erastus Asare Donkor dan jarida ne mai binciken kwakwaf a Ghana, ya shaidawa DW cewa a nan kusa dai bai hango lokacin kawar da wannan matsala ba la'akari da karfin mutanen da ke cikinta. Wannan lamari mai kama da saka da mugun zare na zama tamkar annoba ko kuma ruwan dare game duniya a nahiyar Afirka, sakamakon yadda batun Ghana ke kamanceceniya da na kasar Afirka ta Kudu a cewar jami'i a Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro ta ISS da ke Afirka ta Kudu Enoch Randy Aikins. Najeriya ma dai ba ta tsira ba daga irin wadannan miyagun ayyuka na bata-gari a kasashen Afirka ba. Wani rahoto da wata cibiyar bincike a kasar Switzerland ta fitar ya nuna cewa a bana kadai, an yi fasakwabrin gwal na biliyoyin daloli daga Afirka zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa kafin sake fitar da shi zuwa sauran kasashen duniya.