Jagoran adawa ya zama sabon shugababn
August 16, 2021Talla
Hakainde Hichilema dan shekaru 59 sau uku yana karawa da Shugaba Edgar Lungu a zaben shugaban kasar, sai a wannan jikon ya samu nasara a zaben wanda aka gudanar da shi a makon jiya, tun farko an yi ta hasashen cewar Edgar Lungu zai fadi a zaben saboda matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi. Jamiyyar PF da ke mulki ta Edgar Lungu ta ce tana nazarin shigar da kara domin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu.