1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hague: Kotun ICC ta wanke William Ruto na Kenya

Kamaludden SaniApril 6, 2016

Kotun shari'ar manyan laifuka ta ICC ta yanke hukuncin zarge-zargen da ake yi wa mataimakin shugaban kasar Kenya Da hannu a tayar da yamutsin siyasa a 2007.

https://p.dw.com/p/1IQ9x
Kenia William Ruto
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

A wani abu da ya baiwa al'ummar kasar Kenya da ma na kasa da kasa da ke bibiyar sharia'ar da kutun ICC take wa mataimakin shugaban kasar Kenya gami da wani da jarida mamaki da shi ne, irin yadda kotun ta yi watsi da zarge-zargen da ake masu na tayar da hankalin daya janyo hasarar rayukan 'yan kasar sama da dubu daya a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekara ta 2007.

Babbar Rijistra a kotun ta ICC Jelena Vukasinovic ta ce:

"A karkashin rinjayen da aka samu na hukuncin, wannan matakin na hukuncin ba ya kunshe da wasu sabbin tuhume-tuhume a nan gaba wala Allah a cikin kotun ta ICC ko kuma wata hukumar shari'a ta duniya, za kuma a iya daukaka wannan hukuncin."

Kenia Prozess gegen William Ruto in Den Haag
Willian Ruto a kotun ICCHoto: Reuters

To amma ga lauyan da ke kare wadanda suka rasa iyalansu da 'yan uwansu sakamakon yamutsin kasar Kenyan Wilferd Nderitu cewa yake.

"An riga an yanke hukunci kuma wannan hukunci ne da ya zama dole mu mutunta,ko shakka babu hukuncin yazo a ba zata kuma tare da bakantawa wadanda suka rasa 'yan uwan su rai."

A yayin da hukucin na ICC ke zuwa ga wadanda suka shigar da karar a bazata da kuma takaici, shi kuwa Josua Sang dan jarida da ke zama daya daga cikin wadanda ake tuhuma maida martani yake a dangane da hukuncin.

"So nake na yi godiyYa gare ku ga Allah,ina matikar godewa 'yan Kenya a bisa irin addu'oin da kuka dinga yima ma a lokuta,ina matikar kaunar ku, yanzu kuma na samu 'yanci."

Kenia Prozess gegen William Ruto Kriegsverbrechen Symbolbild
Hargitsin da ya biyo bayan zaben Kenya a 2007Hoto: picture-alliance/AP Photo

To sai dai masu bibiyar al'amuran shari'ar kotun irin su Agina Owang cewa yake.

"Hukuncin alkalan ICC sun gaza ta yin la'akari da yadda aka yanke hukuncin kuma an yi amfani da shi ne a domin dalilan siyasa don zama darasi ga zabubbukan da za su iya zuwa nan gaba, a hannu daya kuma ya sanya damuwa ga wadanda suka shigar da karar, a inda suka yi fatan Icc zat a share musu hawaye,to amma hukunci yayi nesa da irin yadda suke gani."

Kotun da ICC dai ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake wa William Ruto mataimakin shugaban kasar Kenya mai shekaru 49 a duniya da Josua Song mai shekaru 40 a bisa rashin kwararan shaidu daga bangaren da suka shigar da karar to sai dai ta ce za aiya daukaka kara.