Hadari jirgin kasa ya halaka mutane 50 a Indiya
October 19, 2018Talla
Ana kyautata zaton kusan mutane 50 sun halaka sakamakon hadarin jirgin kasa a arewacin kasar Indiya. Akwai kuma wasu mutane kimanin 60 da suka jikata sakamakon lamarin.
Rahotanni sun ce jirgin ya yi karo da kayayyakin biki na al'adun Hindu lokacin da yake tafiya tsakanin wasu manyan birane na arewacin kasar. Tuni Firaminista Narendra Modi na kasar ta Indiya ya nuna takaicin abin da ya faru, inda ya ce gwamnati za ta taimakin mutanen da lamarin ya shafa.