Habasha ta kori jamian diplomasiya na kasar Norway
August 28, 2007Talla
Gwamnatin kasar Habasha ta kori wasu jamian diplomasiya 6 na kasar Norway.Gwamnatin tace ta kori wadannan jamian ne saboda ganin cewa shiga tsakani da Norway takeyi a rikicin bakin iyaka kasar da Eritrea zai kasance wata barazan ce ga harkokin tsaro na kasar.An bukaci jamian na ofishin jakdancin Norway dasu bar kasar nan zuwa 15 ga watan satumba,wanda hakan zai bar jamian Norway biyu kacal a birnin Addis Ababa.Ministan harkokin wajen Norway Jonas Gahr Stoere yace wannan mataki ya basu mamaki matuka,yana mai baiyana cewa tattaunawa kann batun kan iyaka Habasha da Eritrea ya dogara ne kan yarda tsakanin kasashen biyu.