Sojojin gwamnati za su afkawa Mekele
November 22, 2020Talla
Kakakin rundunar Habasha Dejene Tsegaye ya sanar da cewar, mataki na gaba da ke gabansu shi ne yi wa birnin Mekele kawanya da tankunan yaki. Inda ya gargadi mazauna birnin dubu 500, da su yi kokarin cire wa kansu kitse a wuta tun suna da lokacin haka.
Tun a farkon wannan wata ne dai framinista Abiy Ahmed da ya samu lambar yabo ta Nobel a kan zaman lafiya a bara, ya umurci kaddamar da yaki a kan mayakan fafutukar 'yancin Tigray da ake kira TPLF a takaice, bayan zarginsu da kai hari kan sansanonin sojin gwamnati guda biyu da ke yankin.